✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sauke shugabannin jam’iyyar APC a Zamfara

Babbar Kotu da ke zamanta a Gusau ta rushe shugabancin jam'iyyar APC a dukkan matakan jihar

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ta rushe shugabancin jam’iyyar APC a dukkan matakan jihar.

Wani Alhaji Surajo Garba da wasu mutum 138 abokan siyasar Sanata Kabir Garba Marafa ne suka shigar da karar neman kotun ta soke zaben shugabannin.

Masu karar sun kafa hujjar cewa ba a bi kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba wajen gudanar da zaben na shekarar 2018 da ya kawo shugabancin wadanda ake zargin.

Sun kuma ce ba a basu dama sun shiga zaben ba, don haka suka nemi kotun da ta ayyana shugabannin jami’yyar tun daga matakin mazabu har zuwa na jiha a matsayin haramtattu.

Da yake yanke hukuncin, Mai Sharia Bello Tukur Gummi ya ce ya gamsu da hujjojin da masu shigar da karar cewa ba a yi zaben shugabanin jami’yyar bisa ka’ida ba.

Alkalin ya kuma hana wadanda kotun ta sauke din daga gabatar da kawunansu a matsayin shugabanni jam’iyyar.

Ya kuma umarci a yi sabon zaben shugabannin jamiyar a kuma tabbatar an yi wa kowan adalci ta hanyar bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

To sai dai lauyan shugabannin jam’iyyar APC da hukuncin ya shafa a jihar, Barista Kelechi Odeoyegbo ya ce suna duba yiwuwar daukaka kara.