Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, ta sanya Laraba, 6 ga watan Satumban 2023, a matsayin ranar yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar Zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ce dai ta bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben, amma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar dan takara na jam’iyyar PDP da takwaransa na jam’iyyar Labour, Peter Obi na daga cikin wadanda suka kalubalanci sakamakon zaben.
- Ukraine: Rasha ta sanya makaminta na kare-dangi cikin shirin ko-ta-kwana
- Wasu ’yan siyasa na kokarin shirya wa gwamnatin Tinubu mummunar zanga-zanga – DSS
Atiku ya roki kotu da ta soke nasarar da Tinubu ya samu a kan rashin bin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma Dokar Zabe.
A nasa bangaren, Obi ya roki kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kan cewa an yi aringizon kuri’u da APC ta samu.
A baya dai an sanya 1 ga watan Agusta a matsayin ranar yanke sakamakon shari’ar kamar yadda alkalan kotun sauraron korafe-korafen zaben karkashin jagorancin Haruna Tsammani ya bayyana.
Sai dai kuma a ranar Litinin, Babban Magatakardan Kotun, Umar Bangari Esq, ya tabbatar da cewa kwamitin alkalan mai wakilai biyar ya amince da ranar Laraba a matsayin ranar zartar da hukunci.
Ya ce za a bai wa kafofin watsa labarai damar yada shari’ar kai tsaye.