✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan jadawalin zabe

  Babbar kotun da ke Tirnin Tarayya na Abuja ta tsayar da ranar 25 ga watan Afrilu don yanke hukunci kan karar da jam’iyyar Accord…

 
Babbar kotun da ke Tirnin Tarayya na Abuja ta tsayar da ranar 25 ga watan Afrilu don yanke hukunci kan karar da jam’iyyar Accord ta shigar tana kalubalantar sake fasalin lokutan zaben shekarar 2019 da majalisar dokoki ta tarayya ta yi.
 
Mai shari’a Ahmed Mohammed ne ya tsayar da ranar jiya bayan da lauyan jam’iyyar ya kammala gabatar da hujjojinsa a gaban kotun.
 
Lauyan jam’iyyar Accord, Wole Olanipekun ya nemi kotun ta dakatar da matakin da majalisar ta dauka na yi wa lokutan zaben shekarar 2019 gyaran fuska da yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta tsara tun farko.
 
Ya dage a kan cewa idan aka bar majalisar dokoki suka sauya lokutan zabe sannan kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta dage lokutan zaben  to hakan zai janyo rudani a harkokin zaben kasar nan.
 
Olanipekun ya ce idan aka yi la’akari da hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar bakwai ga watan Mayun shekarar 2016, kotun tana da ikon dakatar da majalisar dokokin wajen aiwatar da karfin ikon da kundin dokokin Najeriya ya ba su na shekarar 1999 ta hawa kujerar-naki tare da ikon yin amfani da kashi biyu bisa uku na membobin majalisar don tabbatar da duk wata doka da shugaban kasa ya ki amince da ita.