Kotu ta tsare jagoran zanga-zangar #RevolutionNow kuma mamallakin jaridar intanet ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore da wasu mutun hudu a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja.
Kotun Majistare da ke zamanta a Wuse, Abuja, ta bayar da umarnin ne yayi sauraron shari’ar zargin su da shirya makarkashiya, gudanar da haramtaccen taro da kuma neman harzuwa jama’a, amma sun musanta zargin.
- Za a kaddamr da aikin sabbin ma’aikata 774,000 ranar Talata
- ’Yan ta’adda sun yi wa mafarauci yankan rago a Abuja
“An tura mu Gidan Yarin Kuje na tsawon awa 24 yayin da suke shirin daukar mataki na gaba,” kamar yadda Sowore ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Alkain kotun, Mabel Segun Bello, ta ce a ci gaba da tsare Sowore da sauran mutum hudun ne har sai ta kammala sauraron bukatarsu ta samun beli.
Kotun da kuma sanya ranar Talata, 5 ga watan janairun 2021 don sauraron bukatar tasu ta samun beli wanda lauyansu, Mashal Abubakar zai gabatar.
An tsare su ne a ranar 31 ga watan Disamba, 2020 a Abuja, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar rashin amince da abin da suka kira rashi shugabanci na gari, aka kuma kai su caji ofis.