Kotun sauraron kararrakin zaben ’yan majalisa ta soke kujerun ’yan majalisar Wakilai na jam’iyyar PDP guda uku a Jihar Filato.
Wadanda hukuncin ta shafa su ne Remvyat Nanbol da Agbalak Adukuchill da Happiness Akawu, masu wakiltar mazabun Langtang ta Tsakiya da Rukuba/Iregwe da kuma Pengana da ke Jihar.
Kotun ta kuma ayyana Daniel Ninbol Listic na LP da Bako Ankala da kuma Yakubu Sanda na APC wadanda suka zo ma biyu a zaben a matsayin sababbin ’yan majalisar.
Da yake yanke hukuncin, jagoran alkalan kotun, Mai Shari’a Muhammad Tukur, ya ce ’yan majalisar da aka dakatar ba su ci takararsu ta halastacciyar hanya ba.
Ta kuma ce sun ki bin umarin wata kotu kan ta shirya manyan tarukanta tun daga matakan mazabu.
Alkalin ya ce a sakamakon haka, shugabancin jam’iyyar ba shi da halaccin da zai tsayar da ’yan takara har su shiga zabuka.
Kotun ta kuma ce masu ƙarar na da damar da za su kalubalanci shigar PDP har aka fafata da ita a zaben.
Shugaban kotun ya kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta janye takardun shaidar lashe zaben da ta ba ’yan majalisar sannan ta bayar da shi ga wadanda ta ayyana.
Aminiya ta gano cewa kotun dai a baya ta soke kujerun majalisar tarayya guda hudu, ciki har da ta Sanata guda daya saboda rikicin jam’iyyar.