A ranar 25 ga Janairu, 2023, Babbar Kotun Abuja za ta yanke hukunci kan shari’ar gidaje 40 da ta ba da umarnin a kwace wadanda aka danganta su da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa, a ranar 4 ga Nuwamba, kotun ta bai wa Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC), umarnin kwace gidajen, ta kuma bukaci hukumar ta wallafa bayanin haka a jarida a cikin kwana bakwai.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Aka Fara Karbar Katin Zaben 2023
- Kirsimeti: An cire shingaye a Hanyar Kano-Abuja
Haka nan, ta ba da damar wanda ke da ja kan umarnin da ta bayar, ya gabatar da korafinsa cikin kwana 14 da wallafa batun a jarida.
Sai dai, babban dan Ekweremadu, Loyd da Gwamnatin Jihar Anambra da kuma kamfanin Uni-medical Healthcare Limited, sun shiga kotu ranar 5 ga Disamba, suna kalubalantar umarnin.
Bayan sauraron lauyoyin duka bangarorin a zaman kotun na ranar Alhamis, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ayyana ranar 25 ga Janairu, 2023 don yanke hukunci.
Sanata Ekweremadu ya shiga garari ne tun bayan da aka kama shi a kasar waje kan zargin safarar sassan mutum.
(NAN)