✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta sa a rataye mutumin da ya kashe matarsa

Kotun ta yanke masa hukuncin kisa a kan laifin da aya aikata a 2016.

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a garin Gumel, Jihar Jigawa ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani magidnaci da ya kashe matarsa, mai suna Rabi’u Mamman.

Kotun ta yanke wa mutumin, wanda mazaunin kauyen Medin Labo, a Karamar Hukumar Gagarawa, hukuncin ne bayan gabatar mata da hujojji game da kisan matarsa.

  1. An dakatar da rigakafin Coronavirus saboda wasu kura-kurai da aka gano
  2. Majalisa ta gindaya sharudan kirkirar sabbin jihohi

Alkalin kotun, Mai Shari’a Abubakar Mohammed Sambo, ya ce kotu ta gamsu da shaidu da kuma bayanan da aka gabatar mata cewa Mamman ne ya kashe matarsa a daji.

Sanarwar da kakakin Ma’aikatar Shari’ar Jihar, Zainab Baba Santali, ta fitar ta ce wanda aka yanke wa hukuncin, ya aikata laifin ne tun a shekarar 2016.

Magidancin, ya ja mai dakin nasa ne cikin daji inda ya yi amfani da sanda ya doke ta a kai, sannan ya haka rami ya binne ta.