✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta raba auren matar da mijinta ya kama da kwarto

Kotun ta raba auren tare da umartar kowa a cikinsu ya kama gabansa.

Wata kotun gargajiya ta raba auren shekara 15 bayan mijin ya kama matarsa da kwarto a gidansa.

Da take yanke hukuncin, alkalin kotun da ke zamanta a Ikole-Ekiti,  Yemisi Ojo, ta yanke hukuncin raba auren saboda kawo kwarto da cin amana da mijin ke wa matar tasa.

Da yake gabatar da kara, magidancin mai shekara 36, ya shaida wa kotun cewa yana neman ta raba auren ne saboda ya sha kama matar tasa da kwarto kuma ba ta taba nuna nadama ba.

Bugu da kari, “Ta dade tana yi wa rayuwata barazana,“ inji shi.

Amma da take kare kanta, matar mai shekara 25, ta musanta zarge-zargen tare da cewa “Ban taba yi masa barazana ba ko matar da ke dauke da cikinsa barazana ba, sannan ban yarda a raba auren ba, saboda dana mai shekara tara”.

Bayan sauraron bangarorin ne Misis Ojo datse igiyar auren ta kuma umarci kowanne daga bangarorin biyu ya kama gabansa.

Kotun ta kuma sa magidancin ya dauki dansu mai shekara tara ya ci gaba da daukar nauyin karatunsa.

Ta kuma umarci magidancin da ya rika barin dan yana ganin mahaifiyarsa.