Wata Kotu ta kashe auren wasu magidanta saboda rashi daidaiton sha’awawar matar da mijinta.
Kotun Yankin da ke zamanta garin Jos, Jihar Filato, ta raba auren ne saboda abin da alkalin ya kira bambancin da ba zai daidaitu ba.
- Tsadar hatsi na neman fin karfin mutane a Kaduna
- Makwabcina ya yi wa ’yata cikin shege
- Nuna tsiraici: Bidiyon sabuwar wakar Hausa ya ta da kura a intanet
- Mu waiwayi batun camfi a rayuwar Hausawa
Matar ta shigar da kara ne da cewa, “Bukatar mijina ta jima’i ta wuce misali, ba zan iya ci gaba da wannan aure ba.”
Ta shaida wa kotun cewa saboda karfin sha’war mijin nata, “ba ya raga min wajen bukatar jima’i ko’ina cikin jinin al’ada.”
A don haka Alkali Lawal Suleiman, ya amsa bukatar matar ta raba auren, sannan ya umarce ta da ta dawo wa mijin nata da sadakin N25,000 da ya biya.
Ya kuma umarci mijin daya rika biyan ta kudin kula da ’yar da suka haifa a kowane wata.
Sannnan ya yi mishi kashedin cewa rashin yin haka zai zama raina kotu ne wanda zai fuskanci hukunci mai tsanani.