✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta nemi a kamo Jay-Jay Okocha

Babban Kotun jihar Legas ta bukaci a gaggauta kamo mata tsohon Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya, Super Eagles Austin Jay-Jay Okocha don ya…

Babban Kotun jihar Legas ta bukaci a gaggauta kamo mata tsohon Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya, Super Eagles Austin Jay-Jay Okocha don ya fuskanci hukunci a kan rashin kin biyan haraji na tsawon lokaci.

Alkalin Kotun Mai shari’a Adebayo Akintoye ne ya bayar da wannan umarni a shekaranjiya Laraba a wata takarda da ya fitar mai dauke da sanya hannunsa inda kafofin watsa labarai suka samu kwafe.

Okocha wanda yana daga cikin ’yan kwallon da suka daukaka martabar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a lokacin da yake buga mata kwallo, kotun ta bayar da umarnin a kamo shi ne bayan ta nemi ya gurfana a gabanta a lokuta daban-daban amma dan kwallon ya yi biris da wannan bukata.

Hakan ya sa a shekaranjiya Laraba kotun ta umarci a kamo shi don ya fuskanci shari’a bayan ta dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan gobe (Afrilu).

Sai dai a nasa bangaren Okocha wanda bai dade da dawowa daga kasar Sifen a kan wata harka da ta kai shi can ba, ya yi mamakin umarnin da kotun ta bayar na a kamo shi.

Ya ce a iya saninsa, kotun ba ta taba aika masa wata takardar gayyata don ya gurfana a gabanta ba, sai dai kawai ya ga sammaci ana nemansa ruwa a jallo wanda hakan ya yi matukar ba shi mamaki.

Ya ce ganin yadda ya bauta wa kasar nan a bangaren kwallon kafa, bai dace a yi masa haka ba.

Sai dai a nata bangaren, kotun ta ce idan aka zo batun shari’a ba sani ba sabo, don haka duk wanda ya taka doka, tilas ya gurfana gaban shari’a.

Gwamnatin Jihar Legas ce a karkashin Hukumar Kula Tara Kudaden Shiga ta Jihar (IRS)  ta kai karar Jay-Jay Okocha bayan ya dauki tsawon lokaci ba tare da ya sanar da gwamnati kudin shigar da yake samu daga kamfanoninsa da ke hulda a jihar ba, wanda hakan ya sa ya dauki tsawon lokaci ba tare da ya biya haraji ba, kuma hakan ya saba wa dokar biyan haraji a jihar.