✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta mika gidajen Diezani 56 ga gwamnati

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta mika wa Gwamnatin Tarayya gidaje 56 da ake zargin tsohuwar Ministan Man fetur Misis Diezani Alison-Madueke ta…

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta mika wa Gwamnatin Tarayya gidaje 56 da ake zargin tsohuwar Ministan Man fetur Misis Diezani Alison-Madueke ta saya a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2013 da kudinsu ya haura Naira biliyan uku da miliyan 320.

Alkalin Kotun Mai shari’a Abdulaziz Anka, wanda ya bayar da umarnin a matsayin na wucin-gadi,ya bayar da umarnin ne a ranar Talatar da ta gabata, sakamakon bukatar haka da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gabatar a ranar 16 ga Agusta.

Mai shari’a Anka ya ba Hukumar EFCC damar ta nada wanda zai kula da gidajen tare da bai wa wadda ake kara kwana 14 ta nuna abin da zai hana a mika wa Gwamnatin Tarayya gidajen kacokan ba.

Alkalin ya kuma umarci hukumar ta buga wannan umarni a kowacce daga cikin jaridun kasar nan tare da daga sauraren shari’ar zuwa 8 ga Satumba.

Ana karar Diezani da Donald Chidi Amamgbo da kuma kamfanoni hudu da suka hada da – Chapel Properties Limited da Blue Nile Estate Limited da Azinga Meadows Limited da kuma bistapoint Property Debelopment Limited da hada kai wajen zamba da almundahanar kudi.

Lauyan EFCC, Mista Anselem Ozioko ya shaida wa Mai shari’a Anka cea, Misis Alison-Madueke ta biya Dala miliyan 16 da dubu 441 da Senti 906 (kimanin Naira biliyan 2 da miliyan 600) lakadan a lokutan daban-daban da kuma Dala miliyan 5 da dubu 540 da Senti 318 (kimanin Naira miliyan 840) lakaadn don sayen gidajen ta amfani da kamfanonin ‘giri’ wadanda ainihin nata ne.

 Kamfanonin su ne; Chapel Properties da Blue Nile Estate da Azinga Meadows da kuma bistapoint Property Debelopment.

Ozioko ya ce hukumar ta gano an yi amfani da kamfanoni 14  ga tsohuwar Ministar domin kula mata da wadannan gidaje. Kuma ya ce ta sayi wadannan gidaje ne da kudin haram a lokacin da take Minista.

Kadarorin sun hada da: Gidaje 29 masu dakuna hurhudu da rukunin gidaje shida masu dakuna uku-uku da gidajen kasaita biyu masu dakuna uku-uku da tawagyen gidaje biyu da gida mai dakunan kwana hudu da wani gida a Lamba 7  Thurnbull Street and 5, Raymond Street, Yaba da gidaje 16 a Heritage Court Estate, Plot 2C, Omerelu Street, Diobu, GRA Phase 1 Edtension, Fatakwal da gidaje 13 masu dakunan kwana uku-uku da gidajen alfarma shida masu dakuna uku-uku da sashin yaran gida dai-dai da wurin wasan kwallon Tennis da wurin motsa jiki da kuma “lambun manya.” Dukan gidajen ana zargin ta saye su ne ta amfani da kamfanonin da aka ambata.

Misis Alison-Madueke ta sha musanta wadannan zarge-zarge.