✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta mallaka wa gwamnati kadarorin Diezani

Wata Babbar Kotun da ke Legas ta mallaka wa Gwamnatin Tarayya kaddarorin tsohuwar Ministar Man Fetur, Misis Diezani Alison-Madueke da suka kai Dala miliyan 40,…

Wata Babbar Kotun da ke Legas ta mallaka wa Gwamnatin Tarayya kaddarorin tsohuwar Ministar Man Fetur, Misis Diezani Alison-Madueke da suka kai Dala miliyan 40, kimanin Naira biliyan 14.

Kotun ta mallaka wa Najeriya wani katafaren gidan Misis Diezani da ke yankin Tsibirin Banana Island a Legas, wanda kudinsa ya kai Dala miliyan 37 da rabi, kimanin Naira biliyan 13.

Alkalin Kotun Mai shari’a Chuba Obiozor ya kuma mallaka wa gwamnatin sama da Naira miliyan 84 da kuma sama da Dala miliyan biyu, wasu kudin da aka karba a matsayin na haya na gidan na Banana Island.

A kwanan baya kotun ta bai wa gwamnatin damar kwace kadarorin na wucin-gadi, bayan Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta nemi kotun ta mallaka wa gwamnati kadarorin.

Bayan haka ne kotun ta ba da umarnin a buga hukuncin a jaridu, domin duk wanda ke da wani dalili da zai sa ba za a mallaka wa gwamnati kadarorin na dindindin ba ya kawo dalilinsa a gaban kotun.

A zaman da aka yi ranar Litinin, Lauyan Hukumar EFCC, Anselem Ozioko, ya shaida wa kotun cewa hukumar ta yi biyayya ga hukuncin kotun. Ya ce duk da cewa an mika wa masu ruwa-da-tsaki a lamarin hukuncin kotun na bai wa gwamanti damar kwace kadarorin, babu wanda ya bayyana a kotun domin kalubalantar umarnin na kotun na kwace su.

Rashin dalilin ne ya sa kotun ta mallaka wa gwamantin kadarorin na dindindin.

Ba wannan ne karo na farko ba da aka kwace kadarorin tsohuwar Ministar, domin a watan Afrilun bara, Hukumar EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai Naira miliyan 593 daga hannunta.

Ana zarginta da sacewa da kuma yin facaka da kudin kasar nan a lokacin da take Minista, koda yake ta sha musanta zargin.

A watan Fabrairun bana wata Babbar Kotun Tarayya ta amince a halatta tare da mallaka wa gwamnati kudaden da aka samu daga wajen Diezani Allison-Madueke.