Kotu ta kwace kudaden tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ta saboda ya kasa bayanin yadda ya same su.
Kudaden da Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin kwacewan sun hada da Dala 613,192.49 da kuma Naira miliyan 24.3 a asusun ajiyar Abdulaziz Yari daban-daban a Bankin Zenith.
- Buhari ya nada sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro
- Majalisa ta hana kashe N10bn kan sayo rigakafin COVID-19
- An kone gidaje a artabu tsakanin jami’an tsaro da ’yan IPOB a Imo
- ‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’
Kotun da ke zamanta a Gusau ta kuma kwace Dala 56,056 da ke asusun ajiyar tsohon gwamnan a Bankin Polaris duk ta mallaka wa Gwamnatin Tarayya.
Alkalin Kotun, Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta yanke hukuncin ne a ranar Talata yayin sauraron shari’ar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Zamba (ICPC) ta gurfanar da tsohon gwamnan.
Alkalin ta ce Yari ya kasa bayar da gamsassun dalilan da za su hana kotun amincewa da bukatar ICPC na kwace kudaden.
Babu bayanin yadda ya samu kudaden
ICPC ta kai shigar da karar ce tana bukatar a mallaka wa Gwamnatin Tarayya kudaden da ta gano a wurin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara daga 2011 zuwa 2019 wanda Hukumar take bincike a kansa.
Hukumar ta yi karar sa ne tare da kamfanoninsa biyu; Kayatawa Nigeria Ltd da kuma B. T. Oil and Gas Nigeria Ltd bisa zargin kudaden an same su ne ta haramtacciyar hanya.
A watan Agustan 2019 Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya ba da umarnin wucin gadi na mallaka wa Gwamnatin Tarayya kudaden bisa kamar yadda lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha ya bukata.
A lokacin Mai Shari’a Taiwo ya bukaci Hukumar ta wallafa a manyan jaridu guda biyu, idan akwai wani da ke kalubalantar a kwace kudaden a mallaka su ga Gwamantin Tarayya.