✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kori karar APC kan kujerar Wudil a Majalisar Kano

Hukuncin wata ’yar manuniya ce a kan gaskiyar nasararsu a zaben tun da farko.

Kotun Sauraron Kararrakin Zabe a Jihar Kano, ta kori karar da jam’iyyar APC ta shigar tana kalubalantar nasarar Abdullahi Ali Wudil na jam’iyyar NNPP wanda ya lashe zaben dan Majalisar Dokokin jihar mai wakiltar Karamar Hukumar Wudil.

Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Bilkisu Gambo Yusuf ce ta yanke hukuncin watsi da korafin Abdullahi Nuhu Achika na jam’iyyar APC kamar yadda wakilyarmu ta ruwaito.

Barista Yusuf Mukhtar wanda shi ne lauyan jam’iyyar NNPP, ya nuna farin cikinsa ga hukuncin kotun ta yanke.

A cewarsa, hukuncin wata ’yar manuniya ce a kan gaskiyar nasararsu a zaben tun da farko.

“Tun bayan da aka yi zabe Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben kuma ta bayyana Abdullahi Ali Wudil a matsayin wanda ya yi nasara.

“Daga nan dan takarar na APC ya kalubalanci nasarar tamu, wanda a dalilin haka Hukumar INEC ta bayar da umarnin sake yin zabe a kan wannan kujera.

“Bayan an sake yin zabe har ila yau shi dai Abdullahi Ali Wudil shi ya sake samun nasara.

“Amma duk da haka sai dan takarar jami’yyar APC ya sake nuna rashin gamsuwarsa a kan wannan nasara.

“A nan ya garzaya kotun sauraron kararrakin zabe don kalubalantar wannan nasara.

“A yanzu kuma sai ga shi gaskiya ta yi halinta, kotun ta sake jaddada mana wannan nasara.”

Sai dai duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin lauyan jami’yyar APC, abin ya ci tura.