Kotun Kundin Tsarin Mulki a Thailand ta kori Firaministan kasar, Prayuth Chan-ocha, daga mukaminsa bayan fara sauraron wani koke kan tsawaita wa’adin mulkinsa na shekara takwas.
Kodayake akwai yiwuwar a dawo da shi kan mukaminsa bayan kammala binciken, amma korar tasa ta jefa siyasar kasar cikin rudani.
- Zan iya tuka mota daga Abuja zuwa Kaduna babu ’yan rakiya – Ministan Buhari
- Miji ya saki matarsa kan yin ‘chatting’ da makwabcinsa
Kotun, a cikin wata sanarwa ranar Litinin ta ce, “Kotun ta yi la’akari da koke da kuma takardun da aka gabatar mata, sannan ta yanke hukuncin cewa batun na bukatar daukar matakin.
“Saboda haka, mafi rinjayen kuri’un da aka kada (biyar daga cikin tara) sun yanke shawarar korar Firaminista daga ranar 24 ga watan Agustan 2022, har sai kotu ta yanke hukuncinta.”
Babbar jam’iyyar adawar kasar ce ta shigar da korafin gaban kotun ranar Litinin, inda ta ce lokacin da Prayuth din ya shafe yana mulkin kasar bayan ya yi juyin mulki a shekara ta 2014, ya kamata a kirga shi a matsayin bangare na shekara takwas din da doka ta tanadar masa.
Korarren Firaministan dai yana da kwana 14 ya kare kansa, inji kotun.
Ta kuma ce korar ta shi ta biyo bayan kada kuri’ar da alkalanta suka yi ranar Laraba.
Sai dai ba a san lokacin da kotun za ta yanke hukunci na karshe ba a kan lamarin.
Daya daga cikin Mataimakan Firaministan Prawit Wongsuwan, ne zai karbi ragama daga hannun Prayuth har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci.