Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa, Zariya ta ki amincewa ta bayar da belin mutumin da ake zargi da yaudarar ’yar uwarsa tare da mika ta ga masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.
Ana dai zargin Abubakar Halliru ne da mika Binta Mohammed ga masu garkuwa da mutanen.
- AFCON: Shin Najeriya za ta iya lashe Gasar Kofin Afirka?
- Acaba ta fara dawowa Kano saboda yajin aikin ’yan Adaidaita Sahu
Alkalin Kotun, Mai Shari’a Kabir Dabo, ya ce kotu ba za ta bayar da belin ba har sai an saurari shaidu tare da kallon yanayin karfinsu.
Ana tuhumar Abubakar ne karkashin sashe na 246 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Kaduna na shekarar 2017.
Dukkan lauyoyin bangarorin biyu sun bayyana wa kotun cewa a shirye suke don ci gaba da shari’ar.
Wanda ake zargin dai ya musanta aikata aikata laifin da ake zarginsa da aikatawar.
Kotun dai ta tsayar da ranakun 24 da 25 ga watan Janairun 2022 don ci gaba da sauraron shaidun bangaren masu kara.
Tunda farko dai, kotu ta ba da belin Abubakar Haliru wadda aka janye belin nasa a ranar 31 ga watan Oktoban bara, biyo bayan korafe-korafen jama’a da ya kaure a wasu kafafen yada labarai.