Babbar kotun Abuja ta ki amincewa da bukatar da Sanata Dino Melaye ya shigar akan janye masa jami’an ‘yan sandan da aka girke a gidansa.
Sanata Dino ya shigar da karar ne ta hanyar Lauyansa Nkem Okoro don ba shi cikakken ‘yancin da dokar kasa ta tanadar.
A yau ne dai kotun zata ci gaba da sauraren karar da Sanatan ya shigar akan tabbatar masa da ‘yancin da doka ta tanadar masa.