Kotu Musulunci ta katse igiyar auren ’yar Gwamnan Kano, Asiya-Balaraba Ganduje, ta kuma umarce ta ta mayar wa tsohon mijinta, Alhaji Inuwa Uba, sadakinsa na N50,000
A ranar Alhamis Babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Filin Hoki a Jihar Kano ta datse igiyar auren Asiya-Balaraba Ganduje da mijinta nata.
- Kotu ta aike da Murja zuwa gidan yari
- An tsare malamai 6 kan tilasta wa dalibai kwaikwayon jima’i a Kenya
Alkalin kotun, Mai Shari’a Khadi Abdullahi Halliru ya bayyana cewa kotun ta yanke igiyar aure tsakanin ma’auratan biyu bisa Khul’i, inda ya umarci Asiya ta mayar wa tsohon mijin nata sadakinsa na Naira dubu hamsin.
Asiya Ganduje ce dai ta nemi kotun da ta datse igiyar aurenta da mijin nata inda ta shaida wa kotun ta bakin lauyanta Barista Ibrahim Aliyu Nassarawa cewa ta yi haka ne a karkarshin Sashen Shari’ar Musulunci wato Khul’i wanda ya ba mata damar fansar kansu daga mazajensu.
Tun a zaman baya lauyoyinta sun shaida wa kotun cewa za su mayar wa wanda suke kara sadakinsa na Naira dubu hamsin.
Amma lauyansa Barista Umar I. Umar ya ce, idan har mai tana son fansar kanta, to dole ta dawo masa da kayayyakinsa da ke wurinta da suka hada da takardun karatunsa da satifike-satifiket da kuma motocinsa.
Haka kuma dole ta sarayar da hakkinta na hadakar wani kamfanin shinkafa.
Amma alkalin kotun, ya bayyana cewa batun wasu kayayyaki da wanda ake kara ya sanya a matsayin sharadin wata magana ce ta daban amma ba ta cikin tsarin Khul’i kasancewar ba a kansu aka gina auren ba. “Ana gina aure ne a kan sadaki”