✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta kashe auren shekara 21 saboda girki

Wata kotu da ke zamanta a yankin Mapo na Ibadan babban birnin jihar Oyo ta katse igiyar wani aure mai shekara 21 tsakanin saboda matar…

Wata kotu da ke zamanta a yankin Mapo na Ibadan babban birnin jihar Oyo ta katse igiyar wani aure mai shekara 21 tsakanin saboda matar ta ki yi wa mijinta da ’ya’yansu girki tsawon shekara biyu.

Mijin mai suna Ojo Ayeni ya ya kai karar matar tasa mai suna Sade kotu bisa zargin ta da daina yi musu girki shi da ’ya’yansu uku tun shekara ta 2018.

Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Odunade ya yanke igiyar auren da nufin a sami zaman lafiya, ya kuma umarci mijin da ya ci gaba da rike biyu daga cikin ’ya’yan, ita kuma matar ta ci gaba da rike karamin cikinsu.

Ya kuma umarci mijin da ya rika biyan N10,000 duk wata a matsayin kudin abincin yaran.

Da yake bayar da shaida a gaban kotun tun da farko, Mista Ojo ya ce a duk lokacin da ya kai karar ta wajen iyayenta kan rashin kyautawa sai ta yi watsi da shi.

Ya ce, “Mai girma alkali, matsalar ta kara tabarbarewa ne lokacin da ta fara yi min dariya duk lokacin da ta gan ni ina yi wa yara girki.

“A zahirin gaskiya a ’yan kwanakin nan ma wata sabuwar dabi’a ta dauka ta dawowa gida da tsakar dare, wanda hakan ya kuma jawo gagarumar baraka a gidan.

“Ta dalilin halayenta har hawan jini ne ya kama ni. Ba zan iya ba gaskiya, na gaji”, inji Ojo.

Sai dai da ta ke mayar da martani, matar ta amince a raba auren amma ta musanta duk zarge-zargen da mijin ya yi mata.

“Gaskiya ne ba na yi wa mijina girki. Na daina yi ne tun lokacin da ya zarge ni da yunkurin zuba masa guba a ciki”, inji Sade.