Wata Babbar Kotu Tarayya a Kano ta haramta wa hukumar da ke karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar binciken tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan bidiyon dala.
Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa hukumar karɓar korafe-korafen ba ta da ikon ta gayyaci tsohon gwamnan game da bidiyon dala.
Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ne ya yanke hukuncin ranar Talata a ƙarar da Ganduje ya shigar kan hukumar ta PCACC.
- Dalilin da mummunan yanayi ke daɗa tunkaro Nijeriya — Majalisar Wakilai
- Rundunar Sojin Kasa ta yi ƙarin haske kan fargabar juyin mulki
Ana iya tuna cewa, a watan Yulin bara ne Ganduje ya shigar da ƙara yana neman kotun ta yi wa ’yancinsa shamaki kan bincikarsa game da bidiyon na dala.
Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban hukumar karɓar korafe-korafen, Muhyi Magaji Rimin Gado ya gayyace shi da ya bayyana domin amsa tambayoyi kan zargin karɓar na goro da ake yi wa tsohon gwamnan.
Sai dai kotun ta ba da umarnin hana gayyata ko kuma bincikar Ganduje wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa har sai abin da kotu ta tsayar a ƙarshe.
Mai shari’a Liman bayan ya yi nazari sosai kan batutuwan da aka gabatar, ya ce laifin da ake zargin Ganduje ya aikata da kuma binciken da hukumar ta yi, laifi ne na tarayya.
Alkalin kotun ya yi fashin baki da cewa laifin gwamnatin tarayya shi ne duk wani nau’in laifi da ke ƙunshe cikin wani ƙuduri da majalisar dokokin kasar ta kafa kuma shugaban kasa ya sanya wa hannu ta zama doka.
Mai shari’a Liman ya ce saboda haka hukumar ta PCACC ba ta da hurumin gayyatar Ganduje kan laifukan da ya kamata hukumomin tarayya kamar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa (EFCC) binciken su.
A shekarar 2018 ce Jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a lokacin da Ganduje yake gwamna.
Tun a wancan lokaci, bidiyon ya nuna shi yana karɓar damun daloli daga hannun wani ɗan kwangila, lamarin da Ganduje ya musanta da cewa haɗa bidiyon aka yi.
Lauyan hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe, Usman Fari ya ce ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin kotun ta yanke hukunci a ƙarar da aka shigar tun Yulin bara, inda ya ce tuni ya samu izinin wanda yake karewa domin ɗaukaka ƙara.
Lauyan Ganduje, Mathew Burkaa SAN, ya ce hukuncin kotun ya tabbatar da matsayinsa cewa hukumar ba za ta iya yin bincike kan wanda yake karewa ba kan wata doka da ke ta tarayya.