✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana Gwamnatin Tarayya riƙe kuɗin ƙananan hukumomin Kano

APC na zargin an tafka maguɗi a zaɓen ƙananan hukumomin Kano da aka gudanar a watan Oktoban 2024.

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta haramta wa Gwamnatin Tarayya riƙewa ko kuma yi wa kuɗaɗen ƙananan hukumomi 44 na jihar katsalandan.

Mai Shari’a Musa Ibrahim Muhammad ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, biyo bayan ƙarar da wakilan ƙananan hukumomin jihar suka kai na kare ‘yancinsu na cin gashin kai dangane da kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayyar ke ware musu.

Wannan shari’ar dai ta samo asali ne bayan da jam’iyyar adawa ta APC ta nemi kotu da ta dakatar da bai wa ƙananan hukumomin jihar kuɗaɗe, bisa zargin tafka maguɗi a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a watan Oktoban 2024.

Aminiya ta ruwaito cewa, Shugaban  Jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas ne ya jagoranci shigar da ƙarar wadda take ƙalubalantar wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Asusun Raba Kuɗi na Tarayya (FAAC), da kuma dukkan ƙananan hukumomi 44 na Kanon.

Sai dai kuma hukuncin da babbar kotun Kano ta yanke ya tabbatar da haƙƙin ƙananan hukumomi na karɓar kudadtensu, tare da hana gwamnatin tarayya ko wasu hukumominta riƙe kuɗaɗen .

A watan Nuwambar bara ce dai Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi, Ibrahim Muhammad ya jagoranci tawagar masu shigar da ƙara ta hannun lauyansu, Bashir Yusuf Muhammad, suna neman kotun ta hana riƙewa ko jinkirin sakin kuɗin ƙananan hukumomin jihar.