✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana DSS tsare Shugaban INEC

Kotu ta ce ta gamsu da bayanan da Yakubu ya gabatar mata.

Babbar Kotu Birnin Tarayya ta dakatar da karar da aka shigar gabanta neman tsige Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu daga mukaminsa kan zargin ba da bayanan karya dangane da kadarorinsa.

Alkalin Kotun, M. A. Hassan, ya ce bayanan gaskiya Yakubu ya bayar dangane da kadarorin da ya mallaka kuma daidai da doka, don haka ya ki amincewa da karar da aka shigar kan shugaban na INEC.

A zaman kotun na ranar Laraba, alkalin ya hana hukumar DSS da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB) kama Yakubun.

Ya yanke hukuncin ne bayan karar da wani mai suna da Somadina Uzoabaka ya shigar da Yakubu da kuma Babban Lauyan Kasa, yana neman Shugaban INEC ya ajiye mukaminsa ya koma gefe har zuwa lokacin da za a kammala binciken tuhume-tuhumen da ke kansa.

Mai karan ya kuma bukaci kotu ta haramta wa Yakubu rike kowane irin mukamin gwamnati na tsawon shekara 10.

Da yake maida martani kan karar, Farfesa Yakubu, ya gabatar wa kotun cikakkun bayanai da hujjojin da suka tabbatar wa kotun hanyoyin samun kudinsa halastattu ne.