✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana a ba malamin da ya nemi matar aure wayarsa

Kotun Majistare da ke zama a Rijiyar Zaki ta umarci ’yan sanda da su saki mota da katin shaida na Dokta Mas’udu Abdulahi malami a…

Kotun Majistare da ke zama a Rijiyar Zaki ta umarci ’yan sanda da su saki mota da katin shaida na Dokta Mas’udu Abdulahi malami a Kwalejin Koyon Aikin Jinya da ke Bebeji bisa zargin sa da yunkurin zakkewa dalibarsa wacce kuma matar aure ce.

Kotu ta saurari karar cewa malamin ya yi tattaki har zuwa gidan matar da nufin ya zakke mata, inda kuma ta dana masa tarko wanda aka kai ga kama shi.

A zaman kotun lauyoyin malamin sun nemi kotu da ta bayar da motar malamin da wayar hannunsa da kuma katin shaidar aikin malamin.

Sai dai alkalin kotun Mai shari’a Aminu Ibrahim Fagge ya amince da roko biyu na katin shaida da mota amma ya ki amincewa da bukatar bayar da wayar hannu kasancewar an bayyana cewa a ckin wayar tasa akwai sakonnin soyayya da malamin ya rika aike wa dalibar tasa.