Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wani tsohon jami’in Hukumar Kwastam ta Najeriya tare da wasu mutum biyu hukuncin daurin shekara 16, bisa laifin shigo da bindigogi 661 ba bisa ka’ida ba.
Kotun, wadda ke karkashin Mai Shari’a Ayokunle Fajji, ta sami Mahmud Hassan da kamfaninsa, da Oscar Okafor da kuma Donatus Achinulo, da laifin hada baki wajen yin fasakwaurin bindigogin.
- Najeriya A Yau: Masu fasa gidajen yari sun fi mu karfin makamai —Ganduroba
- An gano karin gawarwaki 13 na mutanen da hatsarin kwalekwalen Bagwai ya ci
Sai dai kotun ta wanke, ta kuma sallami daya daga cikin wadanda aka tuhuma, Abdullahi Danjuma. daga dukkan zarge-zargen.
A cikin kunshin tuhume-tuhumen da ake musu dai, Babban Lauyan Gwamnati, kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya zarge su da shigo da makaman daga kasar Turkiyya ta tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas.
Ya ce an shigo da bindigogin ne a cikin wata kwantena mai zurfin kafa 40, wadda aka yi karyar cewa kamaren karfe ne a cikinta.
Takardun bogi
Kazalika, an samu wadanda ake zargin da yin takardun kwantenar na bogi don yin fasakwaurin cikin sauki.
Daga nan sai Kotun ta yi umarnin a damka bindigogin ga Gwamnatin Tarayya.
Kazalika, ta umarci a rufe kamfanin da aka yi amfani da shi wajen fasakwaurin, yayin da ta umarci a ba Gwamnatin Tarayya dukkan kadarorinsa.
Da yake yanke hukunci, Alkalin ya ce laifin da mutanen suka aikata mai girma ne saboda ya shafi tsaron kasa.