Wata Kotun Majistare da ke unguwar Ebute Metta a Jihar Legas ta ba da umarnin tsare wani mutum a gidan yari saboda zarginsa da ake cewa yana kwana a cikin wani taragon lalataccen jirgin kasa.
Mutumin, mai suna Olalekan Ibrahim mai kimanin shekara 45 dai ana zarginsa ne da keta iyaka, ko da yake ya musanta aikata laifin.
- Majalisar Zamfara ta daina zama bayan garkuwa da mahaifin shugabanta
- Kotu ta dakatar da Secondus daga shugabancin PDP
Olalekan dai ya shaida wa kotun cewa yana kwana a cikin taragon jirgin ne saboda ya kasa tara kudin da zai iya kama hayar daki.
“Ya Mai Shari’a, ni da wasu mutane da ba mu da muhalli mun yanke shawarar kwana a cikin taragan lalatattun jiragen kasar da ke harabar Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya da ke Ebute Metta a Legas ne saboda ba mu da kudin kama haya,” inji shi.
Daga nan ne alkalin kotun, Mai Shari’a A. A. Oshoniyi ya bayar da wanda ake zargi beli kan N50,000, amma daga bisani ya ce a daure shi saboda ya gaza cika sharadin belin.
Dan sanda mai shigar da kara, Insfekta O. Kehinde ya shaida wa kotun cewa ’yan sandan da ke tashar jirgin ne suka kama wanda ake zargin saboda ba su amince da take-takensa ba.
Ya kuma roki kotun da basu lokaci domin gabatar da hujjojin da za su gamsar da ita cewa wanda ake zargin ya aikata laifin.
Sai dai alkalin ya bayar da belin Olalekan a kan N50,000 da kuma mutum daya da zai tsaya masa.
Kotun ta kuma ba da umarnin a tsare shi a gidan yarin Kirikiri da ke Legas har zuwa lokacin da zai cika sharudan belin nasa.
Alkalin ya kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa tara ga watan Satumbar 2021.