Wata kotun Majistare da ke zamanta a Jihar Ondo ta yanke wa wani matashin manomi, Ojo Michael hukuncin daurin shekara daya a gidan yari saboda ya kashe saniya.
Saniyar wadda darajarta ta kai N130,000, mallakar wani mutum ne mai suna Abubakar Kareem.
- Kotu ta raba auren shekara 15 saboda cin amana
- Kotu ta sa a yi wa wasu matasa bulala a Kano
- Ba zan daina fim saboda aure ba —Rahama Sadau
- Kotun Koli ta rantsar sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya 72
Ananda aka yanke wa hukuncin, an zarge sa da kashe saniyar da bindigar toka, sannan ya yi awon gaba da ita.
Dan sanda mai gabatar da kara, Sajan Olusola Omolade, ya ce wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 20 ga Disamba, 2020 a yankin Ayede-Ogbese da ke Jihar Ondo.
Ya ce, laifin ya saba da sashe na 290 (9), 450 da 516, na kudin laifuka mai lamba 37, kashi na 1 na Jihar Ondo.
Wanda ake karar, ba tare da bata lokaci ba ya amsa laifin nasa a gaban kotun.
Sai dai ya ce ya dauki hukuncin kashe saniyar ne saboda barnar da ta yi masa a gonansa.
Alkalin kotun, Mai Shari’a B.O Ojo, ta yanke masa hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso, da kuma tarar N50,000.
Daga nan kuma ta ba shi umarnin biyan kudin saniyar da ya kashe N130,000.