Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Zariya ta yanke wa wani saurayi hukuncin zaman kaso na shekara uku ko biyan tarar Naira 60,000 bayan ta same shi da laifin yi wa budurwarsa ciki.
Alkalin Kotun ta Biyu ta Shari’ar Musulunci da ke Sabon Garin Zariya, Mai Shari’a Shitu Umar, ya ce kotun ta samu wanda ake tuguma, Rabiu Ibrahim, da aikata laifuffuka uku, kuma a kansu ta yanke masa hukuncin.
“Laifi na farko shi ne yin soyayya da yarinya ba da sanin iyayenta ba,
“Sai laifi na biyu – yaudara ta hanyar gayyata a bisa dalilin rashin lafiya, inda ya yi amfani da wannan damar ya biya bukatarsa.
“Sai laifi na uku: iyayen Rabi’u sun kai kudi Naira 15,000 don a zubar da cikin kuma kotu ta ajiye kudin a matsayin shaida”, inji alkalin.
Mai Shari’a Shitu Umar ya kuma yi tambaya cewa in har Rabi’u bai aikata laifin ba, me ya sa iyayensa suka kai wannan kudi don a zubar da cikin?
Wannan kara dai saurayin ne ya kai don neman a bi masa hakkin bata masa suna da budurwar ta yi na cewa shi ne ya yi mata ciki har ta haifi da namiji.
Da yake tsokaci a kan hukuncin lauyan wacce ake kara, Khalil Kabir Mantissa, cewa ya yi duk da cewa sun yi nasara amma za su je mataki na gaba don nema wa budurwar hakkin lalata rayuwarta.