Kotun Majistire da ke Kafanchan a jihar Kaduna ta daure wani matashi mai shekara 35 mai suna Abdullahi Sani tare da budurwarsa ‘yar shekara 20, Sarah Paul, bayan kama su da laifin satar kaji guda 64 wadanda suka yanka.
Jami’ar da ta shigar da kara ta karanta tuhumar hadin baki wajen aikata laifi da fasa kyaure da sata, wanda dukka sun saba da sashe na 58 da na 332 da na 270 da kuma na 312 na kundin dokokin penal code na jihar Kaduna.
Yayin da yake karanta hukuncin, Alkali Michael Bawa, ya yanke wa Abdullahi Sani hukuncin daurin zama a gidan gyara halinka na tsawon wata 38, sannan ita kuma Sarah za ta fuskanci zaman wata 13 saboda rawar da ta taka wajen aikata laifin.
Alkalin ya kuma yanke wa Abdullahi tarar N600,000, ita kuwa Sarah za ta biya N200,000 a matsayin diyya.
Tun da farko mai shigar da kara, Sufeto Esther Bishen, ta shaidawa kotu cewa wata mai suna Hilary Garba ta kawo musu rahoton cewa a ranar 21 ga watan Mayun bana, an fasa mata gida cikin dare an kuma sace kajin gidan gona masu kwai da kudinsu ya kama N781,970.
Ta ce an kama Sarah Paul ne yayin da take soya wasu daga cikin kajin.
Ta ce ‘yan sanda sun gano wayoyin hannu da talabijin da janareto da katifu da injin amplifier da dardumar daki da ake zargin duka na sata ne, inda ta roki kotu da ta hukunta su bisa tanade-tanaden sashe na 125 sakin layi na takwas na Kundin Manyan Laifuffuka.