✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure Sadiya Haruna ba tare da zabin tara ba

Ana dai zarginta ne da bata sunan wani mawaki a msana'antar.

Wata kotun majistare da ke zamanta a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano a ranar Litinin ta yanke wa tsohuwar jarumar fina-finan nan ta Kannywood, Sadiya Haruna, hukuncin daurin wata shida ba tare da zabin tara ba.

An dai gurfanar da ita ne a gaban kotun bisa zargin bata sunan wani tsohon saurayinta, kuma mawaki a masana’antar, Isa A. Isa.

A wani bidiyo dai da ta yada a shafinta na Instagram, jarumar ta zarge shi da zama dan luwadi kuma mai neman mata, sannan ya yi yunkurin lalata mata rayuwa.

Kotun dai, kakakashin jagorancin Mai Shari’a Muntari Garba Dandago, ta aike da Sadiyan gidan gyaran hali saboda zargin bata suna.

Idan za a iya tunawa, tsohuwar jarumar ta shiga cacar baki da Isa a shekarar 2019, inda ta zarge shi da saka ta yin auren mutu’a, sannan ta ci gaba da yada bidiyoyinsa a shafin nata na Instagram.

Sai dai jarumin ya musanta dukkan zarge-zargen sannan ya maka ta a gaban kotu kan zargin bata suna.

Ko a makon da ya gabata dai sai da tsohuwar jarumar ta yi zargin wasu ’yan daba na kokarin watsa mata acid (guba) a fuskarta.

Tun lokacin da ta bar masana’antar ta Kannywood dai, Sadiya ta koma sana’ar sayar da ‘kayan mata’, lamarin da mutane da dama ke ganin yadda take tallata kayan karara a kafafen sada zumunta, ya saba da al’adar mutanen Jihar.

Ko a shekarar 2021 ma, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama tsohuwar jarumar inda ta gurfanar da ita a gaban kotu, daga bisani kuma aka yanke mata hukuncin komawa makarantar Islamiyya.