✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure mutumin da ya guntule kunnen kwarto

Babbar Kotu a Jihar Osun ta yanke hukuncin daurin shekara 5 ga Mista Olaniyan Isiah saboda cizon da ya yi sanadin guntile kunne daya na…

Babbar Kotu a Jihar Osun ta yanke hukuncin daurin shekara 5 ga Mista Olaniyan Isiah saboda cizon da ya yi sanadin guntile kunne daya na makwabcinsa da yake zargin yana yi masa kwartanci.

Mai gabatar kara daga Ma’aikatar shari’a ta Jihar Osun, Mista Bamidele Salawu ya ce an tuhumi Mista Olaniyan Isiah ne da yunkurin kisan kai da yin mummunan rauni, wanda laifi ne da ya kamata a hukumta wanda ya aikata shi a karkashin sashe na 320 (1) da 335 da 338 (1) na kundin dokoki a Jihar Osun.

Ya ce, wanda ake zargin, ya aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Yuli na 2015 a garin Ipetumodu a lokacin da yake rike da wata sandar karfe, ya kutsa cikin dakin makwabcinsa Mista Alonge Emmanuel tare da makure wuyan makwabcin tare da far masa da duka saboda yana zargisa da yin lalata da matarsa mai suna Esther.

Mutumin da ake zarginsa da kwartanci ya kubuce zuwa wani gida da Isiah ya bi shi, ya kama shi tare da gartsa masa cizo a kunnensa, inda ya yi sanadiyyar guntile kunnen nasa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Raheem Siyanbola ya ce ya gamsu da irin bayanan mai gabatar da kara ya gabatar a gaban kotun, wanda ya sa ya yanke wannan hukunci na shekara 5 da aiki mai tsanani a gidan yari ga Mista Olaniyan Isiah.

Kafin a yanke hukumcin sai da lauyar da ke kare mai laifi, Uwargida Olatunji Lawal ta roki kotun da ta saukaka hukumci.

An ji cewa matar mai laifin Uwargida Esther ta fice daga cikin gidan da suke zaune da mijinta, kwanaki 4 kafin aukuwar wannan al’amari.