✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure matashi saboda satar wayar abokansa

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zama a Dutse  Jihar Jigawa ta tura wani matashi zuwa gidan yari sakamakon samunsa da laifin satar wayoyin hannu…

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zama a Dutse  Jihar Jigawa ta tura wani matashi zuwa gidan yari sakamakon samunsa da laifin satar wayoyin hannu mallakar abokan kwanansa, a wani shago da ke Sabuwar Kasuwar Dutse.

Da yake amsa tambayoyin alkalin kotun, wanda ake tuhumar, Abubakar Iliya ya musanta laifin da ake tuhumar tasa, bayan da dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotu ya tabbatar da cewar duk abin da ake zargin Abubakar Iliya da aikatawa gaske ne ya aikata.

Mai Sharia Muhammed Adamu ya tabbatar da cewar saboda tirjiyar da wanda ake zargin ya nuna, kotu zata tsare shi a karkashin sashe na 280. Saboda haka za a ci gaba da tsare shi har tsawan mako biyu masu zuwa, domin ’yan sanda su gabatar da shaidarsu a gaban kotu domin ba ta damar yi masa hukuncin da ya dace.

Daya daga cikin masu karar, Malam Dahiru Abdullahi ya ce a shago daya suke kwana da abokin nasu kafin ya sace masu wayoyin, kuma kafin a je wurin ’yan sanda ya tabbatar wa yayansu cewar shi ne ya sace wayoyin. Hakazalika a gaban ’yan sanda ya sake fada da bakinsa cewa shi ya yi satar, sakamakon haka ne aka gabatar da shi a gaban kotu domin a yi masa hukunci.