✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure matan aure 2 a Kaduna saboda cizon juna

Matan biyu sun gwada kwanjin juna tare da ba wa hammata iska.

Wata kotun shari’ar musunlunci da ke Rigasa a Jihar Kaduna, ta daure wasu matan aure biyu saboda ba wa hammata iskar da suka yi.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Salisu Abubakar Tureta, ne ya zartar musu da hukuncin daurin sati biyu a gidan gyaran hali, bayan gano matan biyu sun dambata tare da cizon juna.

Abubakar Tureta, ya ce daurin wani hukunci ne da zai koya musu hankali da kaunar zaman lafiya a tsakaninsu.

Daya daga cikin matan, Azima Usman Tasiu, ce ta shigar da karar kishiyarta, Aisha Tasi’u a gaban kotun kan zargin cizonta.

Azima, ta shaida wa kotun cewar ita ce mata ta uku ga Tasi’u, inda ta kara da cewar kishiyarta ta mata dukan tsiya bayan samun sabani tsakaninta da yaron A’isha.

Sai dai wadda ake tuhumar (A’isha), ta ce Azima ce ta fara takalarta da neman fada sannan kuma ta cije ta a kafada.

Ko da kotun ta bukaci mijin nasu Tasi’u, ya bayar da ba’asin abin da ya faru, sai ya kada baki ya ce ya tarar da su suna fada ne, bai san abin da ya hada su ba.

Tasi’u, ya ce duk hukuncin da kotun ta yanke musu a ranar 28 ga watan Fabrairu, zai iya sa wa ya sauwake musu baki daya.