Wata Kotun Majistare da ke zamanta a garin Osogbo na Jihar Osun, ta daure wata mata bayan kwanaki takwas da haiwuwar jaririya wacce aka kama da zargin aikata dan hali.
Aminiya ta samu rahoton cewa ana zargin matar mai suna Janet Ismail da fasa wani shago inda ta yashi wasu tufafi a cikinsa.
- Limami ne ya sa na kashe mahaifiyata
- Hadimin Gwamnan Katsina ya rasu a taron daurin aure
- Yadda yanayin hazo a Kano ya kawo wa matafiya cikas
- Ganduje ya cancanci yabo kan yaki da rashawa —Tinubu
Mai jegon wacce ta gurfanar gaban kotun a ranar Litinin, ta musanta laifuka biyu da ake zarginta da su na fasa shago da kuma satar kayayyaki a cikinsa.
Jami’in dan sanda da ya shigar da kara a gaban kotu, Sufeta Kayode Adoye, ya ce an kama matar da zargin fasa shagon wata mata mai suna Olalere Iyabo Modinat tare da satar kayan kusan Naira dubu 300.
Sufeta Adoye ya ce laifin da ake tuhumar matar ya saba da sashe na 383, 390 da 413 na kundin laifuka na jihar Osun da aka kaddamar a shekarar 2002.
Lauyan wanda ake kara, Mista Najite Okobe, ya nemi kotun ta ba da belin wadda ake zargin tare da ba da tabbacin ba za ta tsere ba.
Alkalin Kotun Misis Adijat Oloyade, ta ki amincewa da bukatar lauyan wadda ake karar, inda ta umarci a tsare ta a gidan gyaran hali na Ilesa kuma ta sanya 12 ga watan Afrilun 2021 a matsayin ranar ci gaba da sauraron karar.