Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano, ta yanke wa wani dan kasar Kamaru mai suna Wamba Jean-Gaston hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari, bayan samun sa da laifin yin safarar mutane.
Mutanen da dan kasar Kamarun ke kokarin safarar su sun hada da mata uku da maza hudu, wadanda yake kokarin tsallakawa da su zuwa kasashen Turai.
- Yadda ’yan Burkina Faso ke murnar juyin mulkin da aka yi
- Matar da dan uwanta ya mika ta ga masu garkuwa ta ba da shaida a Kotu
Alkalin kotun, Abdullahi Muhammed Liman, ya yanke wa Wamba Jean-Gaston hukuncin ne bayan gabatar masa da laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa, sannan ya amsa ba tare da bata lokaci ba.
Mai shigar da kara kuma jami’in Hukumar Yaki da Fataucin Mutane (NAPTIP), Abdullahi Babale, ya shaida wa kotun cewa an cafke Wamba ne a Jihar Kano yana kokarin tsallakawa da wasu mutum bakwai zuwa kasar Aljeriya, a ranar 10 ga watan Disamba, 2021 kuma ba su da shaidar izinin shigowa Najeriya, wanda hakan ya saba da doka.
Liman ya bayyana damuwa kan yadda ake ci gaba da samun yawaitar safarar mutane, wanda ya ce zai iya barazana ga sha’anin tsaro a nahiyar Afirka da kuma kasashe da dama.
Ya ayyana dan kasar Kamarun a matsayin wata annoba da ka iya tallafa wa ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na kasashen Afirka.