✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure dalibi shekara 50 a kan fyade

Mai Shari’a Abiola Soladoye ta Kotun Laifuka na Musamman a Jihar Legas ta yanke wa wani dalibin Jami’ar Legas, daurin shekara 50 a kurkuku  bisa…

Mai Shari’a Abiola Soladoye ta Kotun Laifuka na Musamman a Jihar Legas ta yanke wa wani dalibin Jami’ar Legas, daurin shekara 50 a kurkuku  bisa laifin yi wa wata daliba ‘yar shekara 19 fyade.

An gurfanar da dalibin ne bisa laifuka uku na fyade da cin zarafi da cutarwa, wadanda suka saba wa Dokar Manyan Laifuka ta Jihar Legas, 2015.

“La’akari da zargi na biyu, an samu Otema da laifin, saboda haka kotu ta yanke masa shekara 50 a gidan yari saboda an gabatar wa kotu tabbatacciyar shaidar”, inji alkalin kotun.

Zargi da aka yi wa mai laifin sun hada da yi wa wata daliba fyade a ranar 31 ga watan Janairu, 2018, a gidansa da ke unguwar Bariga ta Jihar Legas.

Sannan akwai zargin yi wa wata dalibar kuma fyade a DLI da ke Jami’ar tare da dukan ta a fuska da kuma cizonta a baya.

Mai gabatar da kara ya ce, wanda ake zargin ya tambayi dalibar ta nuna masa hanyar da zabi bi zuwa Dakin Taro na Moremi, ya kuma matsa ta shiga motarsa domin ya rage mata hanya.

Da ta shiga sai ya datse kofofin motar ya tafi da ita zuwa DLI inda ya nannaushe ta a fuska ya cije ta a baya, ya kuma ce ta cire kayan jikinta ya dauki hotunanta tsirara.

Mai gabatar da karar ya kira shaidu shida daga ciki har da wadanda aka yi wa fyaden kuma duk suka tabbatar wa kotu cewar ya aikata laifin.

Da take yanke hukunci ranar Litinin, Mai Shari’a Soladoye ta kama Otema da laifin dukan daliba daya, sai kuma laifin yi wa dayar fyade.

Ta ce zargin da daya dalibar ta yi sharri ne, saboda da mutumin ya biya ta N50,000 din da suka yi yarjejeniya da ba ta zarge shi da yi mata fyade ba.

Ta kuma ce, hoton asibiti ya nunana cewar mai kaifin ya naushi fuskarta ya kuma cije ta a baya.

Alkalin ta ce, “Bisa la’akari da zargin da aka yi masa na farko, ba a samu John Osagie Otema da laifi ba saboda akwai shaida mai karfi cewa sun yi zina ne bisa yarjejeniyar za su karu da juna”.