Babbar Kotun Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a A.M Liman, ta dakatar da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP a jihar amsa sunan shugabannin jam’iyyar.
Wannan na zuwa ne bayan karar da lauyan mai kara, Dr. N. A. Ayagi, ya shigar kotu mai dauke da kwanan wata 13 ga Mayu, 2022 wanda kotu ta karba ran 16 ga Mayu, 2022.
- Badakalar N287m: EFCC ta tsare tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilai, Patricia Etteh
- Najeriya ta bukaci Facebook ya rufe shafin IPOB
Umarnin kotun ya nuna cewa, “Domin kauce wa haifar da gibi da rashinn daidaito a jam’iyya, an ba da umarnin kange wadanda ake tuhuma, mutum na 3 zuwa na 420, dga amsa sunan shugabannin PDP na Jihar Kano har sai kotu ta saurari karar da ke gabanta.
“A bayar da umarnin sauya takardu da sauran bayanan karar ga mutum na uku zuwa na 42 da ke zargi, sannan a ba da su ga mutumin da ake zargi na 25 ko kuma kaiwa ofishinsa,” inji umarnin kotun.
Alhaji Bello Gambo Bichi, ya shigar da kara ne yana tuhumar jam’iyyar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kuma Kwamitin Gudanarwa na PDP a Jihar Kano.
Babbar Kotun ta tsayar da 24 ga Mayun 2022 a matsayin ranar da za ta saurari karar.