Wata Babbar Kotu a Jihar Benuwe ta dakatar da Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Babbar Kotun ta bayar da umarnin wucin gadi, inda ta haramta wa Dokta Ayu “bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.”
- Jihohi 12 da Abuja da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet
- An zaɓi Musulmi shugaban gwamnatin Scotland
Alkalin Kotun, Mai Shari’a W.I Kpochi ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin bayan sauraron kunshin karar da aka shigar mai lamba MHC/85/2023.
Tun a ranar Juma’ar da gabata ce jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da shugabanta na kasa, Iyorchia Ayu bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.
Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke Karamar Hukumar Gboko, a Jihar Benuwe ne suka dauki matakin.
Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kada kuri’ar rashin kwarin gwiwa kan ayyukansa.
A lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin suka cimma, sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Vanger Dooyum ya ce zagon-kasa da Ayu da kuma na kusa da shi suka yi wa PDP ne ya janyo mata shan kaye a gundumar da kuma jihar baki daya, a zaben gwamna.
Sun kuma zargi Ayu da rashin biyan kudaden da ake karba na shekara-shekara daga ’ya’yan jam’iyyar, kamar yadda dokokinta suka tanada.
Shugabannin PDP a gundumar, su 12 daga cikin 17 ne suka sanya hannu kan takardar dakatar da shugaban na PDP.