Babbar Kotun Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a gidan yari.
Kotun wadda ta yanke hukuncin a wannan Juma’ar, ta ba da umarnin tsare tsohon Gwamnan na CBN a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, babban birnin kasar.
- Yadda aka dauki haramar yanke hukuncin Zaben Gwamnan Kano
- Ba za mu karɓo bashin ketare don cike gibin Kasafin Kudin 2024 ba — Ministan Kudi
Kotun ta kuma dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba, inda za ta bayyana matsayarta kan bukatar beli da tsohon Gwamnan Babban Bankin ya gabatar.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ce ta gurfanar da tsohon Gwamnan bankin a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume shida.
An gurfanar da Emefiele a gaban mai shari’a Hamza Muazu, inda lauyansa Matthew Burkaa, SAN ya gabatar da bukatar neman beli, amma Rotimi Oyedepo, lauyan EFCC, ya nuna adawa da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya.
Bayan sauraron hujjojin kowane bangaren, Mai shari’a Muazu ya ce yana bukatar lokaci kadan don yin nazari a kan bukatar da Emefiele ya kawo ta neman beli.