✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka dauki haramar yanke hukuncin Zaben Gwamnan Kano

Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna na dakon hukuncin kotun.

A yau Juma’a ce Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukunci kan tankiyar da ta dabaibaye zaben gwamnan Kano.

An dai gudanar da zaben ne tun a wata Maris, inda Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai daga bisani jam’iyyar APC ta garzaya Kotun Sauraron Kararrakin Zabe, tana mai neman a sake nazari kan lamarin, inda ta samu nasara kotun ta ce dan takararta, Nasiru Yusuf Gawuna ya lashe zaben.

Kan haka ne NNPP ta garzaya Kotun Daukaka Kara tana mai neman hakki, inda bayan sauraron korafi da hujjojin kowane bangaren a makon jiya, ta ce za ta sanar da hukuncin a wannan Juma’ar.

%d bloggers like this: