Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce ba gaskiya ba ne labarin da ake yadawa kan cewa gwamnatinsa za ta kashe Naira biliyan 6 wajen rabon abincin buɗa baki a wannan wata na Azumin Ramadana.
Gwamnan ya yi watsi da jita-jitar ce cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa, naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari da casa’in da bakwai da dubu saba’in gwamnatinsa ta ware domin aikin ciyarwar sabanin yadda ake ikirari.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan aka rika cece-kuce bayan bullar rahoton cewa gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan shida a matsayin kudin da za ta kashe wajen rabon abincin azumi.
Dangane da hakan ne Gwamnan Kano ya yi kira ga kafofin watsa labarai da su rika tabbatar da sahihancin bayanai gabanin watsa wa al’umma.
A cewar gwamnan, “na lura a ’yan kwanakin da suka gabata akwai rade-radin da ke yawo a kafafen yada labarai masu zargin gwamnatinmu da ware naira biliyan shida a matsayin kudin da za ta kashe don aikin ciyarwa a watan Ramadan.
“Ina so in fito karara in bayyana musu cewa hakikanin adadin kudin da za a kashe a wannan aikin na ciyarwa shi ne naira biliyan daya da miliyan dari da casa’in da bakwai da dubu dari bakwai.
“Ina shawartar kafafen yada labarai da su tabbatar da cewa sun samu alkalumansu game da ayyukanmu daga majiyoyin da suka dace ba tare da fitar da rahotanni kan hasashe ba,” in ji shi.