✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta dakatar da Lewandowski wasa uku jere a La Liga

An bai wa Lewandowski katin gargadi ne har sau biyu.

Kotun Wasanni ta Sifaniya ta hukunta dan wasan gaban Barcelona Robert Lewandowski ta hanyar dakatar da shi wasanni uku a jere.

An bai wa Lewandowski jan kati a wasan da Barcelona ta yi da Osasuna gabanin tafiya hutun Gasar Kofin Duniya da aka fara a watan Nuwamba.

Wata kotu a Madrid ce ta dakatar da hukuncin da aka yi masa a makon jiya, wanda hakan ya bai wa dan wasan damar buga wasan da suka yi canjaras da Espanyol 1-1 a ranar Asabar.

Yanzu dai dan kasar Poland din mai shekara 34 ba zai buga wasan da Barcelona za ta yi ba da Atletico Madrid da Getafe da kuma Girona.

An bai wa Lewandowski katin gargadi ne har sau biyu, na biyu bayan wata mahangurba da ya yi wa David Garcia a fuska, a wasan da suka yi nasara a kan Osasuna da ci 2-1.

Hukumar Kwallon Kafa ta Sifaniya ce ta kara ma shi wasanni biyu kai tsaye, saboda rashin da’ar da ya rika nuna wa alkalin wasa a fafatawar.

Espanyol sun fusata da hukuncin kotun da ya bai wa dan wasan damar buga wasan da suka fafata, abin da ya janyo shugaban kungiyar da wasu manyansu suka ki halartar wasan nasu da Barcelona.