Babbar Kotun Jihar Kano ta dakatar da jam’iyyar NNPP daga korar da ta yi wa dan takararta na Shugaban Kasa a zaɓen da ya gabata, Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kotun, wacce Mai Shari’a Usman Na’Abba ya jagoranta ranar Litinin, ta zartar da kwarya-kwaryar hukuncin dakatar da korar.
- Hajji badi: NAHCON ta bukaci maniyyata su fara ajiye miliyan 4.5
- NNPP ta kori Kwankwaso gaba daya saboda cin amanar jam’iyyar
Ta kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kada da sake ta yi amfani da korar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci na karshe.
Jam’iyyar NNPP ce dai ta shigar da karar, kuma wadanda ake tuhuma su ne; Boniface O. Aniebonam, Gilbert Agbo Major, Barista Tony Christopher Obioha, Kwamared Ogini Olaposi, Hajia Rekia Zanlaga, Mark Usman, Umar A. Jubril da kuma Alhaji Adebanju Wasiu.
Sauran su ne Alhaji Tajudeen Adebayo, Alhaji Mamoh Garuba, AbdulRasaq Abdulsalam, Barista Abiola Henry Olarotimi, Injiniya Babayo Abdullahi Mohammed, Alhaji Ibrahim Yahaya, Chinonso Adiofu, Sunday Chukwuemeka, Barista Jonathan Chineme Ibeogu da kuma hukumar INEC.
Bugu da kari, kotun ta haramta wa wanda ake karar da abokan huldarsu daga fitar da kowacce irin sanarwa ko yin hira da ’yan jarida har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci.
A makon da ya gabata ne dai Kwamitin Amintattu na jam’iyyar na kasa ya dakatar da Kwankwaso daga jam’iyyar na tsawon wata shida Saboda yi wa jam’iyyar zangon kasa.
Kazalika, wani tsagi na jam’iyyar a ranar Talata ya sanar da korar Kwankwaso daga NNPP gaba daya saboda wancan zargin da kuma karin na karkatar da wasu kudaden fom din ’yan takara a yayin zaben da ya gabata.