Wata babbar kotu a Kano ta dakatar da Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje daga rage albashin mambobin Kungiyar Ma’aikatan Shari’a (JUSUN) na wucin gadi.
Mambobin kungiyar ne dai suka shigar da gwamnan kara a kotu saboda zabtare musu albashin watannin Nuwamba da Disamban 2020.
- Ganduje: Shirin Shekarau da Kwankwaso na ta da kura kan 2023
- ’Yan Kasuwar Kantin Kwari sun koka kan dokar Ganduje
- Gwamnatin Kano ta zaftare albashin ma’aikata
Sun shigar da karar ne a ranar 5 ga Janairu 2021, ta hannun lauyansu, Barista F.I. Umar.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Shari’a Usman Na’abba ya ba da umarnin na wucin gadi ne, inda ya kuma umarci duka bangororin biyu da su martaba yarjejeniyar da suka kulla a ranar 19 ga Disamban.
Daga nan sai ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa 28 ga watan Janairun 2021, don ci gaba da sauraronta.
Da yake tsokaci kan lamarin, shugaban kungiyar JUSUN na jihar, Muktar Rabiu Lawal, ya ce sun dauki matakin shari’a ne domin su kalubalanci rage musu albashin da aka yi.
A cewarsa, a watan Nuwamba an rage wa mambobinsu kudin da suka kai kusan Naira miliyan 41, sannan a Disamba kuma aka zaftare musu miliyan 39.
Sai dai ya ce suna fargabar kafin karshen shekara ragin albashin zai iya kai wa miliyan 300.