Wata Kotun Majistiri da ke zamanta a Lafiya, babban birnin Jihar Nassarawa, ta dage sauraron kara da aka shigar da mawakin siyasa, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, kan zarginsa da neman tunzura al’umma da kuma tayar da hankali.
Karar wanda wani mazaunin garin Mararraba da ke makotaka da Abuja mai suna Muhammad Sani Zangina ya shigar, ya danganta shi ne da wani jawabin taron ’yan jarida da ya ce mawakin ya shirya a Abuja, inda ya bayyana nadamar goyon bayansa ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da zarginsa da wargaza kasar kafin mika ta ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu.
A takardar karar wadda wakilinmu ya samu gani, lauyan mai shigar da karar, Barista Muhammad Barde Abdullahi ya gabatar, ya ce zargin da ake yi wa Rararan da aikatawa, ya saba da doka ta 114 a Kundin Shari’a na penal code.
Sai dai a yayin zaman fara sauraron shari’ar a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba, an sanar da kotun cewa wanda ake zargin bai halarci zaman kotun ba.
Jami’in kotun da aka baiwa takardar gayyata don mikata ga wanda ake zargi, ya shaida wa kotun cewa dogaran mawakin ba su ba shi damar kaiwa gare shi ba, a lokacin da ya yi yunkurin hakan a mazauninsa da ke Abuja, bisa zargin suna cika umarnin uban gidansu ne.
Mai shari’a Maryam Nadabo ta amince da bukatar lauyan mai shigar da karar ta a gabatar da takardar gayyatar ta hanyar likata a jikin gidan mawakin, sannan ta dage ranar fara sauraron shari’ar zuwa 4 ga watan Disamba da ke tafe.