✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dage karar malamin da ake tuhuma da yi wa ‘yar shekara 5 fyade a masallaci

Wata kutu a Ikeja jihar Legas ta bada umarnin ci gaba da tsare wani malami mai suna Abdusalam Salawudden da ake tuhuma da yi wa…

Wata kutu a Ikeja jihar Legas ta bada umarnin ci gaba da tsare wani malami mai suna Abdusalam Salawudden da ake tuhuma da yi wa ‘yar shekara 5 fyade a masallaci

Mai gabatar da karar Olanrewaju Dawud, ta shaida wa kotun cewa malamin wanda aka fi sani da Alfa ya yi wa yarinyar fyaxe ne a harabar masalacin da ke lamba 14 akan hanyar Palace a unguwar Igando a Legas, ta ce na’urar daukar hoton bidiyo da aka sanya a harabar masallacin a boye ta nadi bayanan a lokacin da yake aikata laifin, ta ce yarinyar ‘yar shekaru 5 na karkashin kulawar malamin ne. Ana saran bangaren Alfa Abdusalam Salawudeen ya musanta aikata laifin.

Alkaliyar kotun mai shari’a Abiola Soladoye, ta bada umarnin ci gaba da tsare malamin kuma ta dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Oktoba 2019.