✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ci tarar ‘yan sanda N10m kan tsare dan kasuwa a Anambra

Kotu ta ci 'yan sandan tara ne saboda tsare Ekwueme ba bisa kai'da.

Wata babbar kotu mai zamanta a Awka, babban birnin Jihar Anambra, ta ci tarar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Naira miliyan 10 saboda tsare wani dan kasuwa, Chukwuemeka Ekwueme, ba bisa ka’ida ba.

Tarar ta shafi Mataimakin Sufeto-Janar, Abutu Yaro, wanda shi ne mai kula da harkokin ‘yan sanda a shiyya ta 13.

Da yake yanke hukunci yayin zaman kotun a ranar Talata, Mai Shari’a D.A. Onyefulu, ya kuma dora wa ‘yan sanda biyan N200,000 ga mai karar a matsayin kudin shari’a.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito Alkalin ya ba da umarnin kada ‘yan sanda su yi wa Ekwueme wata barazana ko tsare shi a kan batun da ya yanke hukunci.

Hukuncin ya biyo bayan karar da Ekwueme ya shigar kotun mai lamba A/Misc 461/2022 inda ya nemi kotu ta kwato masa ‘yancinsa a wajen ‘yan sanda.

Tun da farko, lauyan Ekwueme, Cif Alex Ejesieme (SAN), ya shaida wa kotun cewa ‘yan sanda sun tsare tare da rike wanda yake karewa tsakanin 14 zuwa 28 ga Disamba, 2022 ba tare da sun kai shi kotu ba.

Ya ce ‘yan sanda sun tsare Ekwueme ne kan batun da ke da alaka da gini a wani filin da ke kusa da Babban Filin Jirgin Saman Oba da ke yankin Karamar Hukumar Idemili ta Kudu a jihar.

(NAN)