Wata Kotu a birnin New York na Amurka, ta ci tarar tsohon shugaban kasar, Donald Trump dala miliyan 355 tare da sanya masa takunkumi a harkokin kasuwancinsa.
A Juma’ar da ta gabata ce wani alkali a New York ya zartas da hukunci cewa dole ne Donald Trump ya biya tarar dala miliyan dari uku da hamsin da hudu, da dubu dari tara (354.9).
Bayanai sun ce hakan dai wani koma baya ne ga tsohon Shugaban na Amurka, wanda wannan shari’a ke barazana ga harkarsa ta gine gine.
Baya ga tarar, an kuma dakatar da shi daga duk wata harkar kasuwanci a New York na tsawon shekaru uku.
Alkali Arthur Engoron ya kuma haramta wa Trump zama wani jami’i ko darakta a kowane irin kamfani a New York har na tsawon shekaru uku.
A karar, wadda Atoni Janar ta New York Letitia James ta gabatar, an tuhumi kamfanonin Trump da iyalinsa da laifin shara karya wajen bayyana dukiyarsu, da karin dala biliyan 3.6 a shekara guda har na tsawon shekaru 10 saboda su yaudari bankuna su ba su basuka bisa sharuɗa masu sauki.
Lauyar da ke kare Trump, Alina Habba, ta ce wannan ba kan Trump kawai zai tsaya ba muddin aka bar wannan hukuncin a haka, saboda haka za su ɗaukaka karar.
A cewarta, “wannan hukuncin zai zama wata alama ga kowane Ba’amurke cewa birnin New York ya daina zama wurin kasuwanci.”