✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta ci Sheikh Abduljabbar tarar Naira miliyan 10

An kuma dora wa Abduljabbar tarar Naira dubu 100 wanda lauyansa, Shehu Dalhatu zai biya gwamnatin Kano.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta ci tarar malamin nan na Kano, Sheikh Abduljabbar Kabara, Naira miliyan 10 bayan shigar da wata karar neman ’yanci da ya yi, lamarin da kotun ta ce hakan cin mutunci ne ga tsarin shari’a.

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya ba da umarnin a mika kudin da aka ci tarar Abduljabbar ga wadanda aka yi karar, wato Kotun Shari’a ta Kofar Kudu da ke Kano da kuma Gwamnatin Jihar Kano.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Alkali Nwite ya sake dora wa Abduljabbar tarar Naira dubu 100 wanda lauyansa, Shehu Dalhatu zai biya gwamnatin Kano.

A cewar Alkalin, da zarar kotu ta gamsu da wata kara a matsayin cin mutunci ga sha’anin shari’a, kotu tana da hurumin hukunta wanda ya shigar da karar.

Ya kara da cewa, halin da lauyan Abduljabbar ya nuna, hali ne na neman yin nasarar shari’a ko ta halin kaka.

Ya ce shigar da kara mai lamba FHC/KN/CS/185/2022 a Kano da kuma sake shigar da wata mai lamba FHC/ABJ/CS/1201/2022 a Abuja kan batu guda kuma daga lauya daya, abin a yi tir da shi ne.

Ya ci gaba da cewa, karar da Abduljabbar ya shigar a Babbar Kotun Kano da kuma wadda ya shigar a Abuja na neman ’yanci da wanke shi daga laifuffukan da ake zarginsa da su a gaban Kotun Shari’a, duk abu daya ne.

Shigar da karar da Abduljabbar ya yi kan batu guda a kotuna biyu mabambanta da kuma halin da lauyan Abduljabbar din ya nuna, baki daya Mai Shari’a Nwite ya ce hakan ya saba wa tsarin shari’a.

An maka Sheikh Abduljabbar Kabara a kotu ne bisa zargin batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) bayan kuma ya kasa kare kansa a wata mukabala da takwarorinsa malamai bisa zargin da ake yi masa.

(NAN)

%d bloggers like this: