✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta bayar da belin Alhassan Doguwa a kan N500m

Ana tuhumar Doguwa da tayar da hargitsin siyasa da kisan kai.

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano ta bayar da belin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa a kan naira miliyan dari biyar.

A makon jiya ne wata Kotun Majistare da ke zamanta a Unguwar Nomansland ta Jihar Kano, ta tura Alhassan Doguwa gidan wakafi.

A yayin zaman kotun na yau Litinin, lauyan wanda ake zargi, Nureini Jimoh (SAN), ya gabatar da bukatar bayar da belin wanda yake karewa a gaban Mai Shari’a Muhammad Nasir Yunusa, bisa hujjar cewa doka ta ba shi wannan ’yanci da kuma cewa Kotun Majistare din ba ta da hurimin tsare shi.

Lauya Jimoh ya gabatar da hujjar cewa tun da wanda ake tuhumar laifukansa sun danganci kisan kai da mallakar makamai ba ba bisa ka’ida ba, Dokokin Shari’a ba su bai wa Kotun Majistare ikon bayar da ajiyar wanda ake tuhumar a gidan kaso ba.

Bayan sauraron wannan dalilai ne, Mai Shari’a Yunusa ya bayar da belin wanda ake tuhuma a bisa sharadin zai gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, kuma dole daya daga cikinsu ya kasance Basarake mai daraja ta daya, yayin da dayan zai kasance Babban Sakatare a Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ko ta jiha

Haka kuma, alkalin ya umarci wanda ake zargin da ya kawo wa kotu dukkan takardunsa na neman izini tafiye-tafiye, wadanda an yi masa rangwamin ba shi dama a kansu idan bukatar hakan ta taso.

A karshe Kotun ta yi wa Doguwa kashedin tsame hannunsa daga shiga mazabarsa yayin duk wata harkalla da ta shafi zaben gwamna da na ’yan majalisar jiha da za a gudanar a karshen wannan makon.

Matashiya

Doguwa mai wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada ya gurfana gaban kuliyar ce bisa zargin wasu laifuka masu alaka da hadin baki wajen aikata kisan kai, da raunata mutane da dama.

Haka kuma, ana zargin Doguwa da hannu a kunna wuta a ofishin jam’iyyar hamayya ta NNPP, wadda ta yi sanadiyyar kona wasu mutane da ke cikin ofishin.

A yayin zaman kotun na ranar Larabar da gabata, wanda ake zargin ya musanta tuhume-tuhumen da suka saba wa sassa na 114 da 221 da 247 na kundin penal kot.

Sai dai kuma Alkalin Kotun, Mai Shari’a Ibrahim Mansur Yola, wanda ya bayar da umarnin ajiye wanda ake zargin a gidan gyaran hali, ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Maris.

Kazalika, a wata sanarwa da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar Talatar makon jiya, ta ce Kwamishinan ’yan sandan jihar da ke lura da al’amuran zaben 2023 CP Muhammad Yakubu ne ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen.

Sanarwar ta ce ana zargin dan majalisar na da hannu a kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu mutum takwas a Karamar Hukumar Doguwa ranar 26 ga watan Fabrairu a lokacin da ake karba tare da tattara sakamakon zaben dan majalisar.

An dai yi ta yada hotuna da bidiyon wasu mutane da ake zargi an harba da bindiga a shafukan sada zumunta.

Tun daga nan kuma rundunar ’yan sandan ta gayyaci dan majalisar domin gudanar da bincike kan batun.

Sanarwar ta ce bayan da dan majalisar ya ki amsa gayyatar ne, rundunar ’yan sandan jihar ta kama shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar.