Wata Babbar Kotu a Jihar Kaduna ta sallami jagoran mabiya darikar Shi’a , Shiekh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenat.
Kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Kurada, ta bayar da umarnin a saki Sheikh El-Zakzaky da mai dakinsa, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu.
- Shari’ar El-Zakzaky da matsarsa: An tsaurara tsaro a Kaduna
- Sabon Salon Karbar Kudin Fansa: Dabara ko Wauta?
Cikin hukuncin da Mai Shari’a Kurada ya yanke a ranar Laraba, ya ce babu wasu kwararan hujjoji da suka tabbatar da zargi takwas da masu tuhumar malamin suka gabatar.
Ana iya tuna cewa, Zakzaky da matarsa sun fuskanci tuhume-tuhume takwas ciki har da na kisan kai, tayar da zauna tsaye da kuma salwantar da dukiyar gwamnati da sauransu.
A karshen shekarar 2015 ce aka kama Sheikh Zakzaky bayan mabiyansa sun yi wata mummunar arangama da dakarun sojin Najeriya a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.